Mark 11:15-19
(Mattiyu 21.12-17; Luka 19.45-48; Yohanna 2.13-22)
15Da suka kai Urushalima, sai Yesu ya shiga filin haikalin, ya fara korar waɗanda suke saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur na masu musayar kuɗi, da kujerun masu sayar da tattabaru, 16ya kuma hana kowa yă ratsa da a filin haikali ɗauke da kayan ciniki. 17Da yake koya musu, sai ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira gidana, gidan addu’a na dukan al’ummai ba’? ▼▼Ish 56.7
Amma ga shi kun mai da shi ‘kogon’yan fashi.’ ▼▼Irm 7.11
” 18Manyan firistoci da malaman dokoki suka ji wannan, sai suka fara neman hanyar da za su kashe shi, gama suna jin tsoronsa, saboda dukan taron suna mamakin koyarwarsa. 19Da yamma ta yi, sai Yesu da almajiransa suka ▼▼Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko suna da ya
bar garin.
Copyright information for
HauSRK