Mark 12:1-12
Misalin’yan haya
(Mattiyu 21.33-46; Luka 20.9-19)
1Sa’an nan ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ya shuka gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa rami domin matsin inabin, ya kuma gina ɗakin gadi. Sai ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, sa’an nan ya yi tafiya. 2Da lokacin girbi ya yi, sai ya aiki wani bawa wajen’yan hayan, don yă karɓo masa’ya’yan inabin daga wurinsu. 3Amma suka kama shi, suka yi masa dūka, suka kore shi hannun wofi. 4Sai ya sāke aikan wani bawa wurinsu, amma suka bugi wannan mutum a kai, suka wulaƙanta shi. 5Har yanzu ya sāke aikan wani. Wannan kuwa suka kashe. Ya aika waɗansu da yawa; suka bubbuge waɗansu, sauran kuwa suka kashe. 6 “Sauran mutum ɗaya da ya rage ya aika, ɗa, da yake ƙauna. Daga ƙarshe sai ya aike shi, yana cewa, ‘Za su girmama ɗana.’ 7 “Amma’yan hayan suka ce wa juna, ‘Aha! Wannan shi ne magājin. Ku zo mu kashe shi, gādon kuma yă zama namu.’ 8Sai suka kama shi suka kashe, suka jefa shi bayan gonar inabin. 9 “To, me, mai gonar inabin zai yi ke nan? Zai zo yă karkashe dukan’yan hayan nan, ya kuma ba wa waɗansu gonar inabin. 10Ba ku taɓa karanta wannan Nassi ba, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi,shi ne kuwa ya zama dutsen kusurwan gini.
11 Ubangiji ya yi wannan,
ya kuma yi kyau a idanunmu’?” ▼
▼ Zab 118.22,23
12Sai manyan Firistoci da malaman dokoki da shugabanni suka nemi hanyar da za su kama shi, domin sun gane ya yi misalin a kansu ne. Amma suka ji tsoron taron, saboda haka suka bar shi suka yi tafiyarsu.
Copyright information for
HauSRK