‏ Mark 12:18-27

Aure a tashin matattu

(Mattiyu 22.23-33; Luka 20.27-40)

18Sa’an nan Sadukiyawa da suke cewa, babu tashin matattu, suka zo masa da tambaya. 19Suka ce, “Malam, Musa ya rubuta mana cewa, in ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata babu’ya’ya, dole mutumin ya auri gwauruwar, yă kuma samo wa ɗan’uwansa’ya’ya. 20To, an yi waɗansu’yan’uwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu babu’ya’ya. 21Na biyun ya auri gwauruwar, sai shi ma ya mutu, babu’ya’ya. Haka kuma na ukun. 22A gaskiya, ba ko ɗaya daga cikin bakwai ɗin da ya bar’ya’ya. Daga ƙarshe, macen ta mutu. 23To, a tashin matattu, matar wa za tă zama, don duk su bakwai nan sun aure ta?”

24Yesu ya ce, “Ashe, ba a cikin kuskure kuke ba saboda rashin sanin Nassi, ko ikon Allah? 25Sa’ad da matattu suka tashi, ba za su yi aure ba, ba kuwa za a ba da su ga aure ba. Za su zama kamar yadda mala’iku suke a cikin sama. 26Game da tashin matattu kuwa, ashe, ba ku karanta a cikin littafin Musa ba, game da labarin ɗan kurmin nan mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, yadda Allah ya yi magana da shi ya ce, ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’?
Fit 3.6
27Shi ba Allah na matattu ba ne, shi Allah na masu rai ne. Kun yi mummunan kuskure!”
Copyright information for HauSRK