‏ Mark 12:28-34

Dokar da ta fi girma duka

(Mattiyu 22.23-33; Luka 20.27-40)

28Wani daga cikin malaman dokoki ya zo ya ji suna muhawwara. Da ya lura cewa Yesu ya amsa musu daidai, sai ya tambaye shi ya ce, “A cikin dukan dokoki, wacce ta fi girma duka?”

29Yesu ya ce, “Wadda ta fi girma duka, ita ce wannan. ‘Ku saurara, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. 30Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.’
M Sh 6.4,5
31Na biyun ita ce, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’
Fir 19.18
Ba wata doka da ta fi waɗannan.”

32Mutumin ya ce, “Malam, ka faɗi daidai. Daidai ne da ka ce, Allah ɗaya ne, babu kuma wani sai shi. 33Nuna ƙauna ga Allah da dukan zuciyarka, da dukan ganewarka, da dukan ƙarfinka, da kuma nuna ƙauna ga maƙwabcinka kamar kanka, ya fi dukan hadayun ƙonawa da sadakoki.”

34Da Yesu ya ga ya amsa da hikima, sai ya ce masa, “Ba ka da nisa da mulkin Allah.” Daga lokacin, ba wanda ya yi karambani yin masa wata tambaya.
Copyright information for HauSRK