Mark 12:35-37
Kiristi ɗan wane ne?
(Mattiyu 22.41-46; Luka 20.41-44)
35Yayinda Yesu yake koyarwa a filin haikalin, sai ya yi tambaya ya ce, “Yaya malaman dokoki suke cewa Kiristi ɗan Dawuda ne? 36Dawuda da kansa ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki ya ce, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,“Zauna a hannun damana
sai na sa abokan gābanka
a ƙarƙashin sawunka.” ’ ▼
▼ Zab 110.1
37 Dawuda da kansa ya kira shi ‘Ubangiji.’ To, ta yaya zai zama ɗansa?” Taro mai yawa suka saurare shi da murna.
Copyright information for
HauSRK