Mark 13:14-23
(Mattiyu 24.15-21; Luka 21.20-24)
14 “Sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama, mai kawo hallaka’ ▼▼ Dan 9.27; Dan 11.31; Dan 12.11
tsaye inda ▼▼Ko kuwa shi; haka ma a aya 29
bai kamata ba (mai karatu ya gane), to, sai waɗanda suke a Yahudiya su gudu zuwa duwatsu. 15Kada wani da yake kan rufin gidansa yă sauka, ko yă shiga gida don yă ɗauki wani abu. 16Kada wani da yake gona kuma yă koma don ɗaukar rigarsa. 17Kaiton mata masu ciki, da mata masu renon’ya’ya a waɗancan kwanakin! 18Ku yi addu’a, kada wannan yă faru a lokacin sanyi. 19Domin waɗancan kwanakin za su zama kwanaki na baƙin ciki, waɗanda ba a taɓa yin irinsa ba tun farkon halitta, har yă zuwa yanzu, ba kuwa za a sāke yin irinsa ba. 20 “Da ba don Ubangiji ya rage kwanakin nan ba, da ba wani da zai tsira. Amma saboda zaɓaɓɓu waɗanda ya zaɓa, sai ya rage kwanakin. 21A lokacin nan, in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko kuwa, ‘Duba, ga shi can!’ Kada ku gaskata. 22Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu. 23Amma ku kula! Na dai gaya muku kome tun da wuri.
Copyright information for
HauSRK