‏ Mark 13:3-13

(Mattiyu 24.3-14; Luka 21.7-19)

3Da Yesu yana zaune a kan Dutsen Zaitun da yake ɗaura da haikali, sai Bitrus, Yaƙub, Yohanna da kuma Andarawus, suka tambaye shi a ɓoye, suka ce, 4“Ka gaya mana, yaushe waɗannan abubuwa za su faru? Wace alama ce kuma za tă nuna cewa, duk waɗannan suna dab da cikawa?”

5Sai Yesu ya ce musu, “Ku lura fa kada wani yă ruɗe ku. 6Da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne shi.’ Za su kuwa ruɗi mutane da yawa. 7Sa’ad da kuka ji labarun yaƙe-yaƙe da jita-jitar yaƙe-yaƙe, kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru. Amma ƙarshen tukuna. 8Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki kuma yă tasar wa mulki. Za a yi girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam, a kuma yi yunwa. Waɗannan dai mafarin azabar naƙuda.

9 “Dole ku yi zaman tsaro. Za a ba da ku ga hukuma, a kuma bulale ku a majami’u. Saboda ni kuma, za ku tsaya a gaban gwamnoni da sarakuna, domin ku ba da shaida a gabansu. 10Dole sai an fara yin wa’azin bishara ga dukan al’ummai. 11Sa’ad da aka kama ku, aka kuma kai ku don a yi muku shari’a, kada ku damu da abin da za ku faɗa. Sai dai ku faɗi abin da aka ba ku a lokacin. Gama ba ku kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.

12 “Ɗan’uwa zai ba da ɗan’uwa a kashe. Mahaifi zai ba da ɗansa.’Ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su. 13Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.
Copyright information for HauSRK