Mark 13:32-37
Ba a san rana ko sa’a ba
(Mattiyu 24.36-44)
32 “Game da wannan rana ko sa’a kuwa, ba wanda ya sani, ko mala’ikun da suke sama, ko Ɗan, sai Uban kaɗai. 33Ku lura fa! Ku zauna a shirye! Don ba ku san lokacin da shi zai zo ba. 34Yana kama da mutumin da zai yi tafiya. Yakan bar gidansa a hannun bayinsa, kowa da nasa aikin da aka sa shi, yă kuma ce wa wanda yake gadin ƙofa, yă yi tsaro. 35 “Saboda haka, sai ku zauna a shirye, domin ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko lokacin da zakara na cara ne, ko kuma da safe ne. 36In ya zo kwaram, kada ka bari yă tarar da kai kana barci. 37Abin da na faɗa muku, na faɗa wa kowa. ‘Ku yi tsaro!’ ”
Copyright information for
HauSRK