Mark 14:12-21
Abincin yamma na Ubangiji
(Mattiyu 26.17-25; Luka 22.7-14,21-23; Yohanna 13.21-30)
12A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, lokacin da akan yanka ɗan ragon hadayar kafara, bisa ga al’ada ta tunawa da Bikin Ƙetarewa, sai almajiran Yesu suka tambaye shi, suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?” 13Sai ya aiki biyu daga cikin almajiransa ya ce, “Ku shiga cikin birni, za ku sadu da wani ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi. 14Gidan da ya shiga, ku gaya wa maigidan cewa, ‘Malam yana tambaya, ina ɗakin baƙina, inda zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina?’ 15Zai nuna muku wani babban ɗakin sama da aka shirya domin baƙi. Ku yi mana shirin a can.” 16Almajiran suka tafi, suka shiga cikin birnin, suka kuwa tarar da kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa. 17Da yamma ta yi, sai Yesu ya zo tare da Sha Biyun. 18Yayinda suke cin abinci a tebur, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗaya daga cikinku zai bashe ni, wani wanda yake ci tare da ni.” 19Suka cika da baƙin ciki, da ɗaya-ɗaya suka ce masa, “Tabbatacce, ba ni ba ne, ko?” 20Ya ce, “Ɗaya daga cikin Sha Biyun ne, wanda yake ci tare da ni a kwano. 21Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda yake a rubuce game da shi, amma kaiton mutumin da ya bashe Ɗan Mutum! Zai fi masa, da ba a haife shi ba.”
Copyright information for
HauSRK