‏ Mark 14:22-26

(Mattiyu 26.26-30; Luka 22.14-23; 1 Korintiyawa 11.23-25)

22Yayinda suke cin abinci, sai Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya, ya ba wa almajiransa, yana cewa, “Ku karɓa, wannan jikina ne.”

23Sai kuma ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, ya kuma miƙa musu, dukansu suka sha daga ciki.

24Sai ya ce musu, “Wannan jinina ne na alkawari, wanda aka zubar da shi saboda mutane da yawa. 25Gaskiya nake gaya muku, ‘Ba zan ƙara sha daga’ya’yan inabi ba, sai ranan nan, da zan sha shi sabo a mulkin Allah.’ ”

26Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.
Copyright information for HauSRK