‏ Mark 14:27-31

Yesu ya yi magana a kan mūsun Bitrus

(Mattiyu 26.31-35; Luka 22.31-34; Yohanna 13.36-38)

27Yesu ya ce musu, “Dukanku za ku ja da baya ku bar ni, gama yana a rubuce cewa, “ ‘Zan bugi makiyayin tumaki,
tumakin kuwa za su warwatse.’
Zak 13.7

28 Amma bayan na tashi, zan sha gabanku zuwa Galili.”

29Bitrus ya ce, “Ko da duka sun ja da baya suka bar ka, ba zan bar ka ba.”

30Yesu ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, yau, tabbatacce, a daren nan, kafin zakara yă yi cara sau biyu
Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko ba su da sau biyu.
kai da kanka za ka yi mūsun sanina sau uku.”

31Amma Bitrus ya yi ta nanatawa da ƙarfi ya ce, “Ko da zan mutu tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Duk sauran ma suka ce haka.
Copyright information for HauSRK