Mark 14:66-72
Bitrus ya yi mūsun sanin Yesu
(Mattiyu 26.69-75; Luka 22.56-62; Yohanna 18.15-18,25-27)
66Yayinda Bitrus yake ƙasa a filin gidan, sai wata yarinya, baiwa, ɗaya daga cikin ma’aikatan babban firist, ta zo can. 67Da ta ga Bitrus yana jin ɗumi, sai ta dube shi da kyau. Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu, Banazare.” 68Amma ya yi mūsu ya ce, “Ban san abin da kike magana ba, balle ma in fahimce ki.” Sai ya fita zuwa zaure. ▼▼Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko suna da ƙofar shiga zakara kuwa ya yi cara
69Da baiwar ta gan shi a can, sai ta sāke gaya wa waɗanda suke tsattsaye a wurin, ta ce, “Wannan mutum yana ɗaya daga cikinsu.” 70Sai ya sāke yin musu. Bayan ɗan lokaci kaɗan, sai waɗanda suke tsattsaye kusa suka ce wa Bitrus, “Lalle, kana ɗaya daga cikinsu, gama kai mutumin Galili ne.” 71Sai ya fara la’antar kansa, yana rantsuwa musu, yana cewa, “Ban san wannan mutumin da kuke magana a kai ba.” 72Nan da nan zakara ya yi cara sau na biyu. ▼▼Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko ba su da sau na biyu.
Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi masa cewa, “Kafin zakara yă yi cara sau biyu, ▼▼Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko ba su da sau biyu.
za ka yi mūsun sanina sau uku.” Sai ya fashe da kuka.
Copyright information for
HauSRK