Mark 15:1-5
Yesu a gaban Bilatus
(Mattiyu 27.1,2,11-14; Luka 23.1-5; Yohanna 18.28-38)
1Da sassafe, sai manyan firistoci da dattawa, da malaman dokoki, da dukan Majalisa, suka yanke shawara. Suka daure Yesu, suka kai shi, suka miƙa shi ga Bilatus. 2Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.” 3Manyan firistoci suka zarge shi a kan abubuwa da yawa. 4Don haka Bilatus ya sāke tambayarsa ya ce, “Ba za ka amsa ba? Dubi abubuwa da yawa da suke zarginka da su.” 5Amma har yanzu, Yesu bai ba da amsa ba, Bilatus ya yi mamaki.
Copyright information for
HauSRK