Mark 15:2-5
2Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.” 3Manyan firistoci suka zarge shi a kan abubuwa da yawa. 4Don haka Bilatus ya sāke tambayarsa ya ce, “Ba za ka amsa ba? Dubi abubuwa da yawa da suke zarginka da su.” 5Amma har yanzu, Yesu bai ba da amsa ba, Bilatus ya yi mamaki.
Copyright information for
HauSRK