‏ Mark 15:21-32

Gicciyewa

(Mattiyu 27.27-30; Yohanna 19.2,3)

21Sai ga wani mutum daga Sairin da ake kira Siman, mahaifin Alekzanda da Rufus, yana wucewa kan hanyarsa daga ƙauye. Sai suka tilasta shi yă ɗauki gicciyen. 22Suka kawo Yesu a wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai). 23Sai suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, don yă rage zafi, amma bai sha ba. 24Sai suka gicciye shi. Suka rarraba tufafinsa, suka jefa ƙuri’a a kansu don su ga abin da kowa zai samu.

25Sa’a ta uku na safe ce kuwa aka gicciye shi. 26Akwai rubutu na zarginsa, da ya ce, Sarkin Yahudawa.

27Suka gicciye’yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗayan kuma a hagunsa.
Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da hagu, 28 Nassin nan kuwa ya cika da ya ce, “An lasafta shi a cikin masu laifi.” (Ish 53.12)
28
Wasu rubuce-rubucen ba su da rubutu a nan. Wasu suna da rubutu mai kama da Luk 22:37.
29Masu wucewa suka zazzage shi. Suka kaɗa kai suna cewa, “To, kai da za ka rushe haikali ka kuma gina shi a kwana uku, 30sai ka sauko daga gicciyen, ka ceci kanka!”

31Haka kuma, manyan firistoci da malaman dokoki suka yi masa ba’a a junansu, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! 32Bari wannan Kiristi, wannan Sarkin Isra’ila, yă sauko yanzu daga gicciye, don mu ga mu kuma gaskata.” Waɗanda aka gicciye tare da shi ma suka zazzage shi.
Copyright information for HauSRK