‏ Mark 15:42-47

Jana’izar Yesu

(Mattiyu 27.57-61; Luka 23.50-56; Yohanna 19.38-42)

42Ranar kuwa ita ce ranar Shirye-shirye (wato, ana kashegari Asabbaci). Saboda haka, da yamma ta yi, sai 43Yusuf daga Arimateya, wani sanannen ɗan Majalisa, wanda dā ma yake jiran zuwan mulkin Allah, ya je wajen Bilatus ba tsoro, ya roƙa a ba shi jikin Yesu. 44Bilatus ya yi mamaki da ya ji cewa Yesu ya riga ya mutu. Sai ya kira jarumin ya tambaye shi ko Yesu ya riga ya mutu. 45Da ya ji ta bakin jarumin cewa haka ne, sai ya ba wa Yusuf jikin. 46Sai Yusuf ya kawo zanen lilin, ya saukar da jikin, ya nannaɗe shi da lilin ɗin, sa’an nan ya sa shi a kabarin da aka fafe a cikin dutse. Sai ya gungura wani dutse ya rufe bakin kabarin. 47Maryamu Magdalin da Maryamu uwar Yusuf sun ga inda aka kwantar da shi.
Copyright information for HauSRK