‏ Mark 15:6-15

(Mattiyu 27.15-26; Luka 23.13-25; Yohanna 18.39–19.16)

6Yanzu fa, al’ada ce a lokacin Bikin, a saki ɗan kurkuku guda wanda mutane suka roƙa. 7Wani mutumin da ake kira Barabbas, yana a kurkuku, tare da waɗansu’yan tawaye da suka yi kisankai a lokacin wani hargitsi. 8Taron suka matso, suka ce roƙi Bilatus yă yi musu abin da ya saba yi.

9Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kuna so in sakar muku Sarkin Yahudawa?” 10Don ya san saboda sonkai ne manyan firistoci suka ba da Yesu a gare shi. 11Amma manyan firistoci suka zuga taron su sa a saki Barabbas, a maimakon Yesu.

12Bilatus ya tambaye su ya ce, “To, me zan yi da wanda kuke ce da shi, sarkin Yahudawa?”

13Suka yi ihu, suka ce, “A gicciye shi!”

14Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?”

Amma suka ƙara yin ihu suna cewa, “A gicciye shi!”

15Don son yă faranta wa taron rai, sai Bilatus ya sakar musu Barabbas. Ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.
Copyright information for HauSRK