Mark 16:1-8
Tashin Yesu daga matattu
(Mattiyu 28.1-8; Luka 24.1-12; Yohanna 20.1-10)
1Da Asabbaci ya wuce, sai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub, da kuma Salome suka sayi kayan ƙanshi domin su je su shafa wa jikin Yesu. 2A ranar farko ta mako, da sassafe, bayan fitowar rana, suna kan hanyarsu zuwa kabarin ke nan, 3sai suka tambaye juna suka ce, “Wane ne zai gungura mana dutsen daga bakin kabarin?” 4Amma da suka ɗaga kai, sai suka ga cewa, an riga an gungura dutsen. Dutsen kuwa babba ne. 5Da suna shiga cikin kabarin, sai suka ga wani saurayi sanye da farar riga, yana zaune a hannun dama, sai suka firgita. 6Ya ce, “Kada ku firgita. Kuna neman Yesu Banazare wanda aka gicciye ne. Ya tashi! Ba ya nan. Ku dubi inda aka kwantar da shi. 7Amma ku tafi ku gaya wa almajiransa da kuma Bitrus cewa, ‘Ya sha gabanku zuwa Galili. Can za ku gan shi, kamar yadda ya faɗa muku.’ ” 8Da rawan jiki da kuma ruɗewa, matan suka fita a guje daga kabarin. Ba su kuwa gaya wa kowa ba, don suna tsoro.
Copyright information for
HauSRK