‏ Mark 2:1-12

Yesu ya warkar da shanyayye

(Mattiyu 9.1-8; Luka 5.17-26)

1Bayan’yan kwanaki, da Yesu ya sāke shiga Kafarnahum, sai mutane suka ji labarin zuwansa gida. 2Mutane suka taru da yawa har ma babu wuri, ko a bakin ƙofa ma, sai ya yi musu wa’azin bishara. 3Waɗansu mutum huɗu suka zo wajensa ɗauke da wani shanyayye. 4Da ba su iya kai shi wurin Yesu ba, saboda taron, sai suka buɗe rufin gidan saman, bisa daidai inda Yesu yake. Bayan da suka huda rami, sai suka saukar da shanyayyen, kwance a kan tabarmarsa. 5Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Saurayi, an gafarta zunubanka.”

6To, waɗansu malaman dokoki da suke zaune a wurin, suka yi tunani a zuciyarsu, suna cewa, 7“Me ya sa mutumin nan yake magana haka? Yana saɓo! Wane ne zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?”

8Nan da nan, Yesu ya gane a ruhunsa abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya ce musu, “Me ya sa kuke tunanin waɗannan abubuwa? 9Wanne ya fi sauƙi, a ce wa shanyayyen, ‘An gafarta zunubanka,’ ko a ce, ‘Tashi, ɗauki tabarmarka ka yi tafiya’? 10Amma don ku san cewa, Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, 11“Ina ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka, ka tafi gida.” 12Sai ya tashi, ya ɗauki tabarmarsa, ya yi tafiyarsa a gabansu duka. Wannan ya ba wa kowa mamaki, suka kuma ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin abu haka ba!”
Copyright information for HauSRK