Mark 2:13-17
Kiran Lawi
(Mattiyu 9.9-13; Luka 5.27-32)
13Yesu ya sāke tafiya bakin tafkin. Taro mai yawa ya zo wurinsa, sai ya fara koya musu. 14Yana cikin tafiya, sai ya ga Lawi, ɗan Alfayus zaune a inda ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai Lawi ya tashi, ya bi shi. 15Yayinda Yesu yake cin abinci a gidan Lawi, sai masu karɓar haraji da “masu zunubi” da yawa, suka zo suka ci tare da shi da almajiransa, gama akwai mutane da yawa da suka bi shi. 16Da malaman dokoki, waɗanda su ma Farisiyawa ne, suka ga yana ci tare da masu “zunubi” da masu karɓar haraji, sai suka tambayi almajiransa, suka ce, “Me ya sa yake ci tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?” 17Da jin wannan, Yesu ya ce musu, “Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya. Ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.”
Copyright information for
HauSRK