‏ Mark 2:18-22

An tuhumi Yesu game da azumi

(Mattiyu 9.14-17; Luka 5.33-39)

18To, almajiran Yohanna da na Farisiyawa suna azumi, sai waɗansu mutane suka zo suka tambayi Yesu, suka ce, “Yaya almajiran Yohanna da na Farisiyawa suna azumi, amma almajiranka ba sa yi?”

19Yesu ya amsa ya ce, “Yaya abokan ango za su yi azumi, sa’ad da yana tare da su? Ai, ba za su yi ba, muddin yana tare da su. 20Ai, lokaci yana zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa’an nan ne fa za su yi azumi.

21 “Ba mai facin sabon ƙyalle a tsohuwar riga. In ya yi haka, sabon ƙyallen zai yage daga tsohuwar, yagewar kuwa za tă zama da muni. 22Ba wanda yakan zuba sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ya yi haka, ruwan inabin zai farfashe salkunan, yă yi hasarar ruwan inabin, salkunan kuma su lalace. A’a, yakan zuba sabon ruwan inabin a sababbin salkuna.”
Copyright information for HauSRK