Mark 3:20-27
Yesu da Be’elzebub
(Mattiyu 12.22-32; Luka 11.14-23; 12.10)
20Sai Yesu ya shiga wani gida, taro kuma ya sāke haɗuwa, har shi da almajiransa ma ba su sami damar cin abinci ba. 21Da’yan’uwansa suka sami wannan labari, sai suka tafi don su dawo da shi, suna cewa, “Ai, ya haukace.” 22Malaman dokokin da suka zo daga Urushalima suka ce, “Ai, yana da Be’elzebub ▼▼Girik Be’ezebowul ko Be’elzebowul
! Da ikon sarkin aljanu yake fitar da aljanu.” 23Sai Yesu ya kira su, ya yi musu magana da misalai ya ce, “Yaya Shaiɗan zai fitar da Shaiɗan? 24In mulki yana gāba da kansa, wannan mulki ba zai tsaya ba. 25In gida yana gāba da kansa, wannan gida ba zai tsaya ba. 26In kuwa Shaiɗan yana gāba da kansa, ya kuma rabu biyu, ba zai tsaya ba, ƙarshensa ya zo ke nan. 27Tabbatacce, ba mai shiga gidan mai ƙarfi yă kwashe dukiyarsa, sai bayan ya daure mai ƙarfin, sa’an nan zai iya yin fashin gidansa.
Copyright information for
HauSRK