‏ Mark 4:1-9

Misalin mai shuka

(Mattiyu 13.1-9; Luka 8.4-8)

1Har wa yau, Yesu ya fara koyarwa a bakin tafki. Domin taron da yake kewaye da shi mai girma ne sosai, sai ya shiga cikin jirgin ruwa, ya zauna a ciki a tafkin, dukan mutanen kuwa suna a gaɓar ruwan. 2Ya koya musu abubuwa da yawa da misalai. A koyarwarsa kuwa ya ce, 3“Ku saurara! Wani manomi ya fita don yă shuka irinsa. 4Da yana yafa irin, sai waɗansu suka fāɗi a kan hanya, tsuntsaye suka zo suka cinye su. 5Waɗansu suka fāɗi a wuri mai duwatsu inda babu ƙasa sosai. Nan da nan, suka tsira domin ƙasar ba zurfi. 6Amma da rana ta taso, sai tsire-tsiren suka ƙone, suka yanƙwane, domin ba su da saiwa. 7Waɗansu irin suka fāɗi a cikin ƙaya. Da suka yi girma sai ƙaya suka shaƙe su, har ya sa ba su yi ƙwaya ba. 8Har yanzu, waɗansu irin suka fāɗi a ƙasa mai kyau. Suka tsira, suka yi girma, suka ba da amfani, suka yi riɓi talatin-talatin, waɗansu sittin-sittin, waɗansu kuma ɗari-ɗari.”

9Sai Yesu ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”
Copyright information for HauSRK