Mark 6:45-52
Yesu ya yi tafiya kan ruwa
(Mattiyu 14.22-33; Yohanna 6.15-21)
45Nan da nan Yesu ya sa almajiransa su shiga jirgin ruwa, su sha gabansa zuwa Betsaida, shi kuma yă sallami taron. 46Bayan ya bar su, sai ya hau kan dutse don yă yi addu’a. 47Da yamma ta yi, jirgin ruwan yana tsakiyar tafkin, Yesu kuma yana can a ƙasa shi kaɗai. 48Ya ga almajiran suna fama da tuƙi saboda iska tana gāba da su. Wajen tsara ta huɗu na dare, sai ya tafi wurinsu, yana takawa a kan tafkin. Ya yi kamar zai wuce su, 49amma da suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai suka yi tsammani fatalwa ce. Sai suka yi ihu, 50domin dukansu sun gan shi, suka kuma tsorata. Nan da nan ya yi magana da su ya ce, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.” 51Sai ya shiga jirgin ruwan tare da su, iskar kuma ta kwanta. Dukansu suka yi mamaki, 52gama ba su fahimci al’amarin burodin nan ba, don zuciyarsu ta taurare.
Copyright information for
HauSRK