‏ Mark 7:1-13

Mai tsabta da marar tsabta

(Mattiyu 15.1-9)

1Farisiyawa da waɗansu malaman dokoki waɗanda suka zo daga Urushalima, suka taru kewaye da Yesu. 2Sai suka ga waɗansu daga cikin almajiransa suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta, wato, da ba a wanke ba. 3(Farisiyawa da dukan Yahudawa ba sa cin abinci, sai sun wanke hannuwa sarai tukuna, yadda al’adun dattawa suka ce. 4Sa’ad da suka dawo daga wurin kasuwanci, dole su wanke hannu kafin su ci abinci. Sukan kuma kiyaye waɗansu al’adu da yawa, kamar wanken kwafuna, tuluna da butoci.
Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko suna da tuluna, butoci da kujeru
)

5Saboda haka, Farisiyawa da malaman dokoki suka tambayi Yesu, suka ce, “Don me almajiranka ba sa bin al’adun dattawa, a maimakon haka suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta?”

6Ya amsa ya ce, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci game da ku munafukai; kamar yadda yake a rubuce cewa, “ ‘Waɗannan mutane da baki suke girmama ni,
amma zukatansu sun yi nesa da ni.
7 A banza suke mini sujada,
koyarwarsu, dokokin mutane ne kawai.’
Ish 29.13

8 Kun yar da umarnan Allah, kuna bin al’adun mutane.”

9Ya kuma ce musu, “Kuna da hanya mai sauƙi na ajiye umarnan Allah a gefe ɗaya, don ku kiyaye al’adunku! 10Gama Musa ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’
Fit 20.12; M Sh 5.16
kuma, ‘Duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.’
Fit 21.17; Fir 20.9
11Amma ku, kukan ce, in mutum ya ce wa mahaifinsa, ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da ya kamata ku samu daga wurina, Korban ne,’ (wato, abin da aka keɓe wa Allah), 12sa’an nan haka ba kwa ƙara barinsa yă yi wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa wani abu. 13Ta haka kuke rushe maganar Allah ta wurin al’adun da kuke miƙa wa’ya’yanku. Haka kuma kuke yin abubuwa da yawa.”
Copyright information for HauSRK