Mark 7:14-23
(Mattiyu 15.10-20)
14Sai Yesu ya sāke kiran taron wurinsa ya ce, “Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimci wannan. 15Ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi. Sai dai abin da ya fita daga cikin mutum ne, yake ƙazantar da shi.” ▼▼Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko suna da “marar tsabta.” 16 Duk mai kunnuwan ji, yă ji
16 ▼▼Wasu rubuce-rubucen ba su da rubutu a nan. Wasu suna da rubutu mai kama da Mrk 4:9, Mrk 4:23.
– 17Bayan ya bar taron, ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi ma’anar wannan misali. 18Ya ce, “Ashe, ba ku da saurin ganewa? Ba ku gane cewa ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi. 19Gama ba ya shiga cikin zuciyarsa, sai dai cikin tumbinsa, sa’an nan kuma yă fita daga jikinsa.” (Da faɗin haka, Yesu ya nuna tsabtar kowane irin abinci.) 20Ya ci gaba, “Abin da yake fitowa daga mutum ne yake ƙazantar da shi. 21Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina, 22kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta. 23Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ƙazantar da mutum.”
Copyright information for
HauSRK