‏ Mark 8:1-10

Yesu ya ciyar da dubu huɗu

(Mattiyu 15.32-39)

1A kwanakin nan wani taro mai girma ya taru. Tun da yake ba su da abin da za su ci, sai Yesu ya kira almajiransa ya ce, 2“Ina jin tausayin mutanen nan, kwanansu uku ke nan tare da ni, kuma ba su da abin da za su ci. 3In na sallame su gida da yunwa, za su kāsa a hanya, don waɗansu daga cikinsu sun zo daga nesa.”

4Almajiransa suka amsa suka ce, “Amma a ina, a wannan wurin da ba kowa, wani zai iya samun isashen burodi, don a ciyar da su?”

5Sai Yesu ya yi tambaya ya ce, “Burodi guda nawa kuke da su?”

Suka ce, “Bakwai.”

6Sai ya gaya wa taron su zazzauna a ƙasa. Bayan ya ɗauki burodin nan bakwai, ya yi godiya, sai ya kakkarya, ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutanen, suka kuwa yi haka. 7Suna kuma da ƙananan kifaye kaɗan, ya ba da godiya dominsu, ya kuma ce wa almajiran su rarraba musu. 8Mutanen suka ci, suka ƙoshi. Daga baya, almajiran suka tattara gutsattsarin da suka rage cike da kwanduna bakwai. 9Wajen maza dubu huɗu ne suka kasance. Da ya sallame su, 10sai ya shiga jirgin ruwa tare da almajiransa, suka tafi yankin Dalmanuta.
Copyright information for HauSRK