Mark 9:14-29
Warkar da yaro mai mugun ruhu
(Mattiyu 17.14-20; Luka 9.37-43)
14Da suka dawo wurin sauran almajiran, sai suka ga babban taro kewaye da su, malaman dokoki suna gardama da su. 15Nan take da dukan mutanen suka ga Yesu, sai suka cika da mamaki, suka ruga da gudu don su gai da shi. 16Ya tambaye su ya ce, “Gardamar me kuke yi da su?” 17Wani mutum a cikin taron ya amsa ya ce, “Malam, na kawo maka ɗana mai wani ruhun da yake hana shi magana. 18Duk lokacin da mugun ruhun ya kama shi, yakan jefa shi a ƙasa. Bakinsa yakan yi kumfa, yă cije haƙorarsa, yakan sa jikinsa ya sandare, yă zama da ƙarfi. Na roƙi almajiranka su fitar da ruhun, amma ba su iya ba.” 19Yesu ya ce, “Ya ku zamani marar bangaskiya, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron.” 20Sai suka kawo shi. Da ruhun ya ga Yesu, nan da nan sai ya buge yaron da farfaɗiya. Ya fāɗi a ƙasa, yana birgima, bakinsa yana kumfa. 21Yesu ya tambayi mahaifin yaron ya ce, “Tun yaushe yake haka?” Ya ce, “Tun yana ƙarami. 22Ya sha jefa shi cikin wuta, ko ruwa don yă kashe shi. Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimake mu.” 23Yesu ya ce, “ ‘In za ka iya’? Ai, kome mai yiwuwa ne ga wanda ya gaskata.” 24Nan da nan mahaifin yaron ya faɗa da ƙarfi ya ce, “Na gaskata, ka taimake ni in sha kan rashin bangaskiyata!” 25Da Yesu ya ga taron suna zuwa can a guje, sai ya tsawata wa mugun ruhun ya ce, “Kai ruhun kurma, da na bebe, na umarce ka, ka fita daga cikinsa, kada kuma ka ƙara shigarsa.” 26Sai ruhun ya yi ihu, ya buge shi da ƙarfi da farfaɗiya, ya fita. Yaron ya kwanta kamar matacce, har mutane da yawa suka ce, “Ai, ya mutu.” 27Amma Yesu ya kama shi a hannu ya ɗaga, ya kuwa tashi tsaye. 28Da Yesu ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi a ɓoye, suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da shi ba?” 29Ya amsa ya ce, “Sai da addu’a ▼▼Waɗansu rubuce-rubucen hannu suna da addu’a da azumi
kaɗai irin wannan yakan fita.”
Copyright information for
HauSRK