‏ Mark 9:30-32

30Suka bar wurin suka bi ta Galili. Yesu bai so wani yă san inda suke ba, 31gama yana koya wa almajiransa. Ya ce musu, “Za a ci amanar Ɗan Mutum, a ba da shi ga hannun mutane. Za su kashe shi, bayan kwana uku kuma zai tashi.” 32Amma ba su fahimci abin da yake nufi ba, suka kuma ji tsoro su tambaye shi game da wannan.
Copyright information for HauSRK