‏ Mark 9:38-40

Wanda ba ya gāba da mu, namu ne

(Luka 9.49,50)

38Yohanna ya ce, “Malam mun ga wani mutum yana fitar da aljanu a cikin sunanka, sai muka ce yă daina, domin shi ba ɗaya daga cikinmu ba ne.”

39Yesu ya ce, “Kada ku hana shi. Ba wanda yake yin ayyukan banmamaki a cikin sunana, nan take yă faɗi wani abu mummuna game da ni. 40Gama duk wanda ba ya gāba da mu, namu ne.
Copyright information for HauSRK