‏ Mark 9:42-48

Sanadin yin zunubi

(Mattiyu 18.6-9; Luka 17.1,2)

42 “Idan kuma wani yă sa ɗaya daga cikin waɗannan’yan yara masu gaskatawa da ni yă yi laifi, zai fiye masa a rataya wani babban dutsen niƙa a wuyarsa, a jefa shi cikin teku. 43In hannunka yana sa ka yin zunubi, yanke shi. Ai, gwamma ka shiga rai da hannu ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta, inda ba a iya kashe wutar ba, da hannuwanka biyu.
Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da fita, 44 inda “tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.”
44
Wasu rubuce-rubucen ba su da rubutu a nan. Wasu suna da rubutu mai kama da Mrk 9:48.
45In kuma ƙafarka tana sa ka yin zunubi, yanke ta. Ai, gwamma ka shiga rai da ƙafa ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da ƙafafunka biyu.
Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da lahira, 46 inda “tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.”
46
Wasu rubuce-rubucen ba su da rubutu a nan. Wasu suna da rubutu mai kama da Mrk 9:48.
47In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi. Ai, gwamma ka shiga mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da idanu biyu, 48inda “ ‘tsutsotsinsu ba sa mutuwa,
wutar kuma ba a iya kashewa.’
Ish 66.24

Copyright information for HauSRK