Matthew 1:1-17
Asalin Yesu Kiristi
(Luka 3.23-38)
1Tarihin da aka rubuta game da asalin Yesu Kiristi ɗan Dawuda, ɗan Ibrahim.2Ibrahim ya haifi Ishaku,
Ishaku ya haifi Yaƙub,
Yaƙub ya haifi Yahuda da’yan’uwansa,
3Yahuda ya haifi Ferez da Zera, waɗanda Tamar ce mahaifiyarsu;
Ferez ya haifi Hezron,
Hezron ya haifi Ram,
4Ram ya haifi Amminadab,
Amminadab ya haifi Nashon,
Nashon ya haifi Salmon,
5Salmon ya haifi Bowaz, wanda Rahab ce mahaifiyarsa,
Bowaz ya haifi Obed, wanda Rut ce mahaifiyarsa,
Obed ya haifi Yesse,
6Yesse kuwa ya haifi Sarki Dawuda.
Dawuda ya haifi Solomon, wanda matar Uriya ce mahaifiyarsa.
7Solomon ya haifi Rehobowam,
Rehobowam ya haifi Abiya,
Abiya ya haifi Asa,
8Asa ya haifi Yehoshafat,
Yehoshafat ya haifi Yehoram,
Yehoram ya haifi Azariya,
9Azariya ya haifi Yotam,
Yotam ya haifi Ahaz,
Ahaz ya haifi Hezekiya,
10Hezekiya ya haifi Manasse,
Manasse ya haifi Amon,
Amon ya haifi Yosiya,
11Yosiya kuma ya haifi Yekoniya ▼
▼Wato, Jehohiyachin; haka ma a aya 12
da’yan’uwansa a lokacin da aka kwashe su zuwa bauta a Babilon.12Bayan an kwashe su zuwa bauta a Babilon.
Yekoniya ya haifi Sheyaltiyel,
Sheyaltiyel ya haifi Zerubbabel,
13Zerubbabel ya haifi Abiyud,
Abiyud ya haifi Eliyakim,
Eliyakim ya haifi Azor,
14Azor ya haifi Zadok,
Zadok ya haifi Akim,
Akim kuma ya haifi Eliyud,
15Eliyud ya haifi Eleyazar,
Eleyazar ya haifi Mattan,
Mattan ya haifi Yaƙub,
16Yaƙub ya haifi Yusuf, mijin Maryamu, wadda ta haifi Yesu, wanda ake kira Kiristi.
17Ta haka akwai zuriya goma sha huɗu ke nan duka-duka daga lokacin Ibrahim zuwa lokacin Dawuda, goma sha huɗu kuma daga Dawuda zuwa bauta a Babilon, goma sha huɗu kuma daga bauta a Babilon zuwa Kiristi. ▼
▼Ko kuwa Kiristi. Kiristi (Da Girik) Almasihu (Da Ibraniyanci) duk suna nufin “Shafaffe.”
Copyright information for
HauSRK