Matthew 1:18-25
Haihuwar Yesu Kiristi
(Luka 2.1-7)
18Ga yadda haihuwar Yesu Kiristi ta kasance. An yi alkawarin auren mahaifiyarsa Maryamu, ga Yusuf. Amma tun kafin su zama miji da mata, sai aka tarar Maryamu tana da ciki, ta wurin Ruhu Mai Tsarki. 19Yusuf mijinta, da yake shi mai adalci ne, bai so yă ba ta kunya, yă tone mata asiri a fili ba, sai ya yi tunani yă sake ta a ɓoye. 20Amma yana cikin wannan tunani, sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana masa cikin mafarki ya ce, “Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukan Maryamu zuwa gidanka a matsayin matarka, gama cikin nan nata, daga wurin Ruhu Mai Tsarki ne. 21Za tă haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, ▼▼Yesu da Girik shi ne Yoshuwa da Ibraniyanci, wanda yake nufin Ubangiji yana ceto.
gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.” 22Duk wannan ya faru ne, don a cika abin da Ubangiji ya faɗi ta bakin annabin cewa, 23“Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, kuma za a kira shi Immanuwel” ▼▼Ish 7.14
(wanda yake nufin “Allah tare da mu”). 24Da Yusuf ya farka daga barci, sai ya bi umarnin mala’ikan Ubangiji, ya ɗauki Maryamu zuwa gida a matsayin matarsa. 25Amma bai kwana da ita ba, sai bayan da ta haifi ɗan. Ya kuwa sa masa suna Yesu.
Copyright information for
HauSRK