Matthew 11:1-19
Yesu da Yohanna Mai Baftisma
(Luka 7.18-35)
1Bayan Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya yi gaba daga can don yă koyar yă kuma yi wa’azi a garuruwan Galili. ▼▼Da Girik a cikin garuruwansu
2Sa’ad da Yohanna Mai Baftisma ya ji a kurkuku abin da Kiristi yake yi, sai ya aiki almajiransa 3su tambaye shi, “Kai ne wanda zai zo, ko kuwa mu sa ido ga wani?” 4Yesu ya amsa ya ce, “Ku koma ku gaya wa Yohanna abin da kuka ji, kuka kuma gani. 5Makafi suna gani, guragu suna tafiya, ana warkar da waɗanda suke da kuturta, kurame suna ji, ana tā da matattu, ana kuma yi wa matalauta wa’azin labari mai daɗi. 6Mai albarka ne mutumin da bai yi tuntuɓe ba saboda ni.” 7Sa’ad da almajiran Yohanna suke barin wurin, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna. “Me kuka je kallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne? 8In ba haka ba, to, me kuka je kallo? Mutum mai sanye da riguna masu kyau ne? A’a, masu sa riguna masu kyau, ai, a fadan sarakuna suke. 9To, me kuka je kallo ne? Annabi? I, ina gaya muku, ya ma fi annabi. 10Wannan shi ne wanda aka rubuta game da shi cewa, “ ‘Zan aiki ɗan saƙona yă sha gabanka,wanda zai shirya hanyarka a gabanka.’ ▼
▼ Mal 3.1
11 Gaskiya nake gaya muku. A cikin dukan waɗanda mata suka haifa, ba wani da ya taso da ya fi Yohanna Mai Baftisma girma; duk da haka mafi ƙanƙanta a mulkin sama ya fi shi girma. 12Tun daga kwanakin Yohanna Mai Baftisma har yă zuwa yanzu, mulkin sama yana sha da ƙyar, fitanannu kuma sun kama mulkin sama sun riƙe gam. 13Gama dukan Annabawa da kuma Doka sun yi ta annabci har yă zuwa kan Yohanna. 14In kuna niyya ku yarda da wannan, to, shi ne Iliya da dā ma zai zo. 15Duk mai kunnen ji, yă ji. 16 “Da me zan kwatanta wannan zamani? Suna kama da yara da suke zaune a kasuwa, suna kiran juna, suna cewa, 17 “ ‘Mun yi muku busa,
ba ku kuwa yi rawa ba,
mun rera waƙar makoki,
ba ku kuwa yi makoki ba.’
18 Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo ba ya ciye-ciye, ba ya shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ai, yana da aljani.’ 19Ɗan Mutum ya zo yana ciye-ciye, yana shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama da kuma mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ Amma akan tabbatar da hikima ta wurin ayyukanta.”
Copyright information for
HauSRK