‏ Matthew 11:20-24

Kaiton biranen da ba su tuba ba

(Luka 7.18-35)

20Sai Yesu ya fara yin tir da biranen da aka yi yawancin ayyukansa na banmamaki, don ba su tuba ba. 21“Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida! Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba sanye da rigar makoki da toka. 22Amma ina gaya muku, za a fi jin tausayin Taya da Sidon a ranar shari’a, fiye da ku. 23Ke kuma Kafarnahum, za a ɗaga ki sama ne? A’a, za ki gangara zuwa zurfafa ne. Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne a aka yi a Sodom, da tana nan har yă zuwa yau. 24Amma ina gaya miki, za a fi jin tausayin Sodom fiye da ke a ranar shari’a.”
Copyright information for HauSRK