‏ Matthew 12:1-8

Ubangijin Asabbaci

(Markus 2.23-28; Luka 6.1-5)

1A lokacin nan Yesu ya bi ta gonakin hatsi a ranar Asabbaci. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara kakkarya kan hatsi suna ci. 2Sa’ad da Farisiyawa suka ga wannan, sai suka ce masa, “Duba! Almajiranka suna yin abin da doka ta hana a yi a ranar Asabbaci.”

3Sai ya amsa ya ce, “Ba ku karanta abin da Dawuda ya yi ba ne sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa? 4Ya shiga gidan Allah, da shi da abokan tafiyarsa suka ci keɓaɓɓen burodin, wanda doka ta hana su yi, sai firistoci kaɗai. 5Ko kuwa ba ku karanta a Doka cewa a ranar Asabbaci firistoci sukan karya dokar Asabbaci duk da haka ba da yin wani laifi ba? 6Ina faɗa muku cewa wani
Ko kuwa a wani abu; haka ma a ayoyi 41 da 42
wanda ya fi haikali yana a nan.
7Da a ce kun san abin da waɗannan kalmomi suke nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba,’
Hos 6.6
da ba ku zargi marar laifi ba.
8Gama Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabbaci.”
Copyright information for HauSRK