‏ Matthew 12:22-30

Yesu da Be’elzebub

(Markus 3.20-30; Luka 11.14-23; 12.10)

22Sai aka kawo masa wani bebe kuma makaho mai aljani, Yesu kuwa ya warkar da shi, har ya iya magana ya kuma sami ganin gari. 23Dukan mutane suka yi mamaki, suka ce, “Wannan Ɗan Dawuda ne kuwa?”

24Amma da Farisiyawa suka ji haka, sai suka ce, “Ahab, da Be’elzebub
Da Girik Be’elzebul Ko kuwa Be’elzebul; haka ma a aya 27
sarkin aljanu ne kaɗai, wannan mutum yake fitar da aljanu.”

25Yesu kuwa ya san tunaninsu sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa zai lalace, kuma duk birni ko gidan da yake rabe gāba da kansa ba zai ɗore ba. 26In Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, ai, ya rabu yana gāba da kansa ke nan. Yaya kuwa mulkinsa zai ɗore? 27In kuwa ta wurin Be’elzebub nake fitar da aljanu, to, ta wa mutanenku suke fitar da su? Saboda haka, su ne za su zama alƙalanku. 28Amma in ina fitar da aljanu ta wurin Ruhun Allah ne, to, fa, mulkin Allah ya zo muku ke nan.

29 “Ko kuwa, yaya wani zai iya shiga gidan mai ƙarfi yă ƙwace masa kaya ba tare da ya fara daure mai ƙarfin nan tukuna ba? Sa’an nan zai iya washe gidansa.

30 “Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni ne, kuma wanda ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.
Copyright information for HauSRK