Matthew 12:9-14
(Markus 3.1-6; Luka 6.6-11)
9Da ya ci gaba daga wurin, sai ya shiga majami’arsu, 10a nan kuwa akwai wani mutum mai shanyayyen hannu. Don neman dalili su zargi Yesu, sai suka tambaye shi suka ce, “Ya dace a warkar a ranar Asabbaci?” 11Ya ce musu, “In waninku yana da tunkiya, ta kuma fāɗa a rami ran Asabbaci, ba zai cire ta daga ramin ba? 12Sau nawa mutum ya fi tunkiya daraja! Saboda haka ya dace a aikata alheri ran Asabbaci.” 13Sa’an nan ya ce wa mutumin, “Miƙa hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye, kamar dai ɗayan. 14Amma Farisiyawa suka fita suka ƙulla shawara yadda za su kashe Yesu.
Copyright information for
HauSRK