Matthew 13:1-9
Misalin mai shuka
(Markus 4.1-9; Luka 8.4-8)
1A ranan nan sai Yesu ya fita daga gida ya je ya zauna a bakin tafkin. 2Taron mutane mai yawan gaske suka taru kewaye da shi har ya kai sai da ya shiga jirgin ruwa ya zauna, yayinda dukan mutane suka tsaya a gaci. 3Sa’an nan ya faɗa musu abubuwa da yawa cikin misalai, yana cewa, “Wani manomi ya fita don yă shuka irinsa. 4Da yana yafa irin, waɗansu suka fāffāɗi a kan hanya, tsuntsaye kuwa suka zo suka cinye su. 5Waɗansu suka fāɗi a wurare mai duwatsu, inda babu ƙasa sosai, nan da nan kuwa suka tsira, da yake ƙasar ba zurfi. 6Sai dai da rana ta ɗaga, sai tsire-tsiren suka ƙone, suka kuma yanƙwane domin ba su da saiwa sosai. 7Waɗansu irin suka fāɗi a cikin ƙaya, ƙayan kuwa ta yi girma ta shaƙe su. 8Har yanzu, waɗansu irin suka fāffāɗi a ƙasa mai kyau, inda suka ba da amfani riɓi ɗari, sittin ko kuma talatin na abin da aka shuka. 9Duk mai kunnen ji, yă ji.”
Copyright information for
HauSRK