Matthew 13:53-58
Rashin ganin darajar annabi
(Markus 6.1-6; Luka 4.16-30)
53Sa’ad da Yesu ya gama ba da waɗannan misalai, sai ya ci gaba daga can. 54Yana isowa garinsa, sai ya fara koya wa mutane a cikin majami’arsu, suka kuwa yi mamaki. Suka yi ta tambaya suna cewa, “Ina wannan mutum ya sami irin wannan hikima da kuma ayyukan banmamaki haka? 55Wannan ba shi ne ɗan kafinta nan ba? Ba mahaifiyarsa ba ce Maryamu,’yan’uwansa kuma Yaƙub, Yusuf, Siman da Yahuda ba? 56Duk’yan’uwansa mata kuma ba tare da mu suke ba? To, a ina wannan mutum ya sami dukan waɗannan abubuwa?” 57Sai suka ji haushinsa. Amma Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa da kuma a gidansa na kaɗai annabi ba ya samun girma.” 58Bai kuwa yi abubuwan banmamaki da yawa a can ba saboda rashin bangaskiyarsu.
Copyright information for
HauSRK