Matthew 14:1-12
An yanke kan Yohanna Mai Baftisma
(Markus 6.14-29; Luka 9.7-9)
1A lokacin nan sarki Hiridus ya ji labarin Yesu, 2sai ya ce wa fadawansa, “Wannan Yohanna Mai Baftisma ne; ya tashi daga matattu! Shi ya sa abubuwan banmamakin nan suke faruwa ta wurinsa.” 3To, dā Hiridus ya kama Yohanna ya daure, ya kuma sa shi cikin kurkuku saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa Filibus, 4gama Yohanna ya dinga ce masa, “Ba daidai ba ne ka aure ta.” 5Hiridus ya so yă kashe Yohanna, amma yana jin tsoron mutane, don sun ɗauka shi annabi ne. 6A bikin tuna da ranar haihuwar Hiridus, diyar Hiridiyas ta yi musu rawa ta kuma gamsar da Hiridus ƙwarai, 7har ya yi alkawari da rantsuwa cewa zai ba ta duk abin da ta roƙa. 8Da mahaifiyarta ta zuga ta, sai ta ce, “Ba ni a cikin kwanon nan, kan Yohanna Mai Baftisma.” 9Sarki ya yi baƙin ciki, amma saboda rantsuwarsa da kuma baƙinsa, sai ya ba da umarni a ba ta abin da ta roƙa 10ya kuma sa aka yanke kan Yohanna a kurkuku. 11Aka kawo kansa cikin kwano aka ba yarinyar, ita kuma ta kai wa mahaifiyarta. 12Almajiran Yohanna suka zo suka ɗauki gawarsa suka binne. Sa’an nan suka je suka gaya wa Yesu.
Copyright information for
HauSRK