‏ Matthew 14:13-21

Yesu ya ciyar da dubu biyar

(Markus 6.30-44; Luka 9.10-17; Yohanna 6.1-14)

13Sa’ad da Yesu ya ji abin da ya faru, sai ya shiga jirgin ruwa ya janye shi kaɗai zuwa wani wuri inda ba kowa. Da jin haka, taron mutane suka bi shi da ƙafa daga garuruwa. 14Da Yesu ya sauka ya kuma ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu ya kuma warkar da marasa lafiyarsu.

15Da yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuma rana ta kusa fāɗuwa. Ka sallami taron don su shiga ƙauyuka su nemi wa kansu abinci.”

16Yesu ya amsa, “Ba su bukata su tafi. Ku ku ba su wani abu su ci.”

17Suka ce, “Burodi biyar da kifi biyu ne kawai muke da su a nan.”

18Ya ce, “Ku kawo mini su a nan.” 19Sai ya umarci mutanen su zazzauna a kan ciyawa. Da ya ɗauki burodi biyar da kifin biyun nan ya dubi sama, ya yi godiya ya kuma kakkarya burodin. Sa’an nan ya ba wa almajiransa, almajiran kuwa suka ba wa mutane. 20Duk suka ci suka ƙoshi, almajiran kuwa suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu. 21Yawan waɗanda suka ci, sun yi wajen maza dubu biyar, ban da mata da yara.
Copyright information for HauSRK