Matthew 15:1-9
Mai tsabta da marar tsabta
(Markus 7.1-13)
1Sa’an nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka zo wurin Yesu daga Urushalima suka yi tambaya suka ce, 2“Me ya sa almajiranka suke karya al’adun dattawa? Ba sa wanke hannuwansu kafin su ci abinci!” 3Yesu ya amsa ya ce, “Ku ma me ya sa kuke karya dokar Allah saboda al’adarku? 4Gama Allah ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, ▼▼Fit 20.12; M Sh 5.16
kuma duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi.’ ▼▼Fit 21.17; Fir 20.9
5Amma ku kukan ce, in wani ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da dā ya kamata za ku samu daga gare ni an ba wa Allah,’ 6ba zai ‘girmama mahaifinsa’ da shi ba. Ta haka kun yi banza da maganar Allah saboda al’adarku. 7Ku munafukai! Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku da ya ce, 8 “ ‘Waɗannan mutane da baki kawai suke girmama ni,amma zukatansu suna nesa da ni.
9 A banza suke mini sujada,
koyarwarsu, dokoki ne kawai da mutane suke koyarwa.’ ” ▼
▼ Ish 29.13
Copyright information for
HauSRK