‏ Matthew 15:10-20

(Markus 7.14-23)

10Sai Yesu ya kira taron wurinsa ya ce, “Ku saurara ku kuma gane. 11Abin da yake shiga bakin mutum ba ya ƙazantar da shi, sai dai abin da yake fitowa daga bakinsa, shi ne yake ƙazantar da shi.”

12Sai almajiran suka zo wurinsa suka ce, “Ka san cewa Farisiyawa ba su ji daɗi sa’ad da suka ji wannan ba?”

13Ya amsa ya ce, “Duk tsiron da Ubana na sama bai shuka ba, za a tumɓuke shi daga saiwoyi. 14Ku ƙyale su, ai, makafin jagorai ne.
Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da jagorai ne na makafi
In makaho ya yi wa makaho jagora, dukansu za su fāɗa a rami.”

15Bitrus ya ce, “Ka bayyana mana wannan misali.”

16Yesu ya tambaye su ya ce, “Har yanzu ba ku gane ba ne? 17Ba ku gane cewa duk abin da ya shiga baki yakan wuce ciki ne daga nan kuma yă fita daga jiki ba? 18Amma abubuwan da suke fitowa ta baki suna fitowa ne daga zuciya, su ne kuma suke ƙazantar da mutum. 19Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa. 20Waɗannan su ne suke ƙazantar da mutum; amma cin abinci ba tare da wanke hannuwa ba, ba ya ƙazantar da mutum.”
Copyright information for HauSRK