‏ Matthew 16:13-19

Shaidar Bitrus a kan Kiristi

(Markus 8.27-30; Luka 9.18-21)

13Sa’ad da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, sai ya tambayi almajiransa ya ce, “Wa mutane suke ce da Ɗan Mutum?”

14Suka amsa, “Waɗansu suna ce Yohanna Mai Baftisma; waɗansu kuma suna ce annabi Iliya; har wa yau waɗansu suna ce Irmiya ne ko kuma ɗaya daga cikin annabawa.”

15Ya tambaye su, “Amma ku fa, wane ne ni a ganinku?”

16Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Kiristi,
Ko kuwa a Almasihu; haka ma a aya 20
Ɗan Allah mai rai.”

17Yesu ya amsa ya ce, “Mai albarka ne kai Siman ɗan Yunana, gama ba mutum ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin sama. 18Ina kuwa gaya maka, kai ne Bitrus,
Bitrus yana nufin dutse.
a kan wannan dutse zan gina ikkilisiyata, kuma ƙofofin Hades
Ko kuwa a lahira
ba za su rinjaye ta ba.
19Zan ba ka mabuɗan mulkin sama; kome ka daure a duniya zai zama a daure a sama, kome kuma ka kunce a duniya zai zama a kunce a sama.”
Copyright information for HauSRK