‏ Matthew 17:1-13

Sākewar kamanni

(Markus 9.2-13; Luka 9.28-36)

1Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna ɗan’uwan Yaƙub, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai. 2A can aka sāke kamanninsa a gabansu. Fuskarsa ta haskaka kamar rana, tufafinsa kuwa suka zama fari fat suna walƙiya. 3Nan take sai ga Musa da Iliya suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.

4Sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. In kana so, sai in kafa bukkoki uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.”

5Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije mai haske ya rufe su, sai wata murya daga cikin girgijen ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!”

6Sa’ad da almajiran suka ji haka, sai suka fāɗi ƙasa rubda ciki, a firgice. 7Amma Yesu ya zo ya taɓa su ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.” 8Da suka ɗaga kai, ba su ga kowa ba sai Yesu kaɗai.

9Suna cikin gangarowa daga dutsen ke nan, sai Yesu ya umarce su cewa, “Kada ku faɗa wa kowa abin da kuka gani, sai bayan an tā da Ɗan Mutum daga matattu.”

10Almajiran suka tambaye shi suka ce, “To, me ya sa malaman dokoki suke cewa, dole sai Iliya ya fara zuwa?”

11Yesu ya amsa ya ce, “Tabbatacce, Iliya zai zo, zai kuma gyara dukan abubuwa. 12Amma ina faɗa muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa gane shi ba, amma suka yi masa duk abin da suka ga dama. Haka ma Ɗan Mutum zai sha wahala a hannunsu.” 13Sa’an nan almajiran suka gane cewa yana musu zancen Yohanna Mai Baftisma ne.
Copyright information for HauSRK