‏ Matthew 17:1-8

Sākewar kamanni

(Markus 9.2-13; Luka 9.28-36)

1Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna ɗan’uwan Yaƙub, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai. 2A can aka sāke kamanninsa a gabansu. Fuskarsa ta haskaka kamar rana, tufafinsa kuwa suka zama fari fat suna walƙiya. 3Nan take sai ga Musa da Iliya suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.

4Sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. In kana so, sai in kafa bukkoki uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.”

5Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije mai haske ya rufe su, sai wata murya daga cikin girgijen ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!”

6Sa’ad da almajiran suka ji haka, sai suka fāɗi ƙasa rubda ciki, a firgice. 7Amma Yesu ya zo ya taɓa su ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.” 8Da suka ɗaga kai, ba su ga kowa ba sai Yesu kaɗai.
Copyright information for HauSRK