Matthew 17:14-18
Warkarwar yaro mai aljani
(Markus 9.14-29; Luka 9.37-43)
14Da suka isa wajen taron, sai wani mutum ya zo ya durƙusa a gabansa. 15Ya ce, “Ubangiji, ka yi wa ɗana jinƙai. Yana da farfaɗiya yana kuma shan wahala ƙwarai. Ya sha fāɗuwa cikin wuta ko ruwa. 16Na kuma kawo shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba.” 17Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku zamani marasa bangaskiya da kuma masu taurinkai, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe kuma zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron a nan.” 18Yesu ya tsawata wa aljanin, ya kuwa rabu da yaron, nan take yaron ya warke.
Copyright information for
HauSRK