‏ Matthew 17:14-20

Warkarwar yaro mai aljani

(Markus 9.14-29; Luka 9.37-43)

14Da suka isa wajen taron, sai wani mutum ya zo ya durƙusa a gabansa. 15Ya ce, “Ubangiji, ka yi wa ɗana jinƙai. Yana da farfaɗiya yana kuma shan wahala ƙwarai. Ya sha fāɗuwa cikin wuta ko ruwa. 16Na kuma kawo shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba.”

17Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku zamani marasa bangaskiya da kuma masu taurinkai, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe kuma zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron a nan.” 18Yesu ya tsawata wa aljanin, ya kuwa rabu da yaron, nan take yaron ya warke.

19Sa’an nan almajiran suka zo wurin Yesu a ɓoye suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da aljanin ba?”

20Ya amsa ya ce, “Saboda kuna da ƙarancin bangaskiya sosai. Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiyar da take ƙanƙanuwa kamar ƙwayar mustad, za ku iya ce wa wannan dutse, ‘Matsa daga nan zuwa can,’ zai kuwa matsa. Babu abin da zai gagare ku.”
Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da kai. 21 Amma irin wannan ba ya fita, sai da addu’a da azumi
Copyright information for HauSRK