‏ Matthew 18:1-5

Mafi girma a mulkin sama

(Markus 9.33-37; Luka 9.46-48)

1A lokacin nan sai almajirai suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, “Wane ne mafi girma a mulkin sama?”

2Sai ya kira ƙaramin yaro ya sa shi yă tsaya a tsakiyarsu. 3Sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in ba kun canja kuka zama kamar ƙananan yara ba, labudda, ba za ku shiga mulkin sama ba. 4Saboda haka, duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar wannan yaro, shi ne mafi girma a mulkin sama. 5Duk kuma wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan a cikin sunana ya karɓe ni ne.
Copyright information for HauSRK